Haramtaciyyar kungiyar yan aware masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, ta musanta cewar tana da hannu a kissan gillar da aka yiwa Harira jibril tare da yaranta guda hudu a Jihar Anambra

Kungiyar tayi Allah wadai da kisan tana mai cewar a kasar igbo, babban laifi ne kashe mace mai juna biyu.

Wasu yan bindiga da ba’asan kosu wanene bane suka hallaka Harira Jubril, da yayanta hudu bayan bude musu wuta a Isulo a karamar hukumar Orumba a ranar Lahadin da ta gabata.

‘Yan bindiga sun kuma shiga wasu unguwannin sun hallaka kimanin mutane biyar.

Karamar hukumar Orumba ta Arewa na ciki kananan hukumomin da gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya saka dokar hana fita daga karfe 6 na safe zuwa 6 na dare cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Gwamna Soludo yayi tir da kisan yana mai cewa bar za’a amince da hakan ba kuma yayi alkawarin binciko wadanda suka aikata don a hukunta su.

Amma, IPOB ta bakin sakatarenta, Emma Powerful, cikin sanarwar daya fitar a karshen makon nan yace wadanda suka kashe bahausiyar da yaranta su saurari abinda zai biyo baya saboda zaluncin da suka yiwa matar da yaranta
Ya jadadda cewar wadanda suka kashe matar ba yan IPOB bane kuma su shirya girbar abinda suka aikata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *