Tsohon shugaban kasa Amurka ya yi kira da a bar malamai su rika yawo a ajujuwan makarantu sakamakon harbin da wani dan bindiga ya yi a wata makarantar Texas a makon nan wanda ya kashe yara 19 da malamai biyu.

Yace:
‘Lokaci ya yi da a ƙarshe za a bar malaman makaranta wadanda suke da isasshen horo su rika yawo da bindiga a makarantu’
‘Trump ya bayyana haka a cikin wani jawabi a yayin wani babban taro na babbar cibiyar harba bindiga ta Amurka, Kungiyar Rifle ta Kasa, a Houston.
Anyi mummunan harbin ne a ranar 24 ga Mayu a Uvalde, Texas yayi da wani matashi mai shekaru 18 sanye da bindiga mai sigar AR-15, ya sake jan hankali kan NRA, babbar mai ba da gudummawa ga membobin Majalisa, galibi ‘yan Republican.