Wata kotu ta yanke hukuncin cewar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana iya yin takarar shugaban kasa a 2023.

Wata kotu a Abuja ta yanke hukuncin cewar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana iya yin takarar shugaban kasa a 2023.

A baya-bayan nan, lauyoyi da masu ruwa da tsaki sun dade suna tafka muhawara kan hallacin shiga takarar Jonathan duba da cewar ya karasa wa’adin Yar’adua sannan ya yi wa’adinsa daya a matsayin shugaban kasa.

Dokar Najeriya ta bada dama ne mutum ya yi tazarce a kujerar shugaban kasa sau biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *