Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana kisan da aka yiwa wata mata mai juna-biyu, Harira Jubril, da ‘ya’yanta hudu a Jihar Anambra a matsayin “dabbaci.

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana kisan da aka yiwa wata mata mai juna-biyu, Harira Jubril, da ‘ya’yanta hudu a Jihar Anambra a matsayin “dabbaci.

A Wata sanarwa da Sakatare Janar na kungiyar, Dr Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar a ranar Alhamis ta ce irin wadannan kashe-kashe na mutanen da basu jiba basu gani ba abin takaici ne.

A cewersa ya kamata gwamnati ta rika daukar matakin gaggawa game da al’amuran tsaro, domin kuwa wannan shi ne babban aikinta kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana.

Ta kara da cewar “JNI tana matukar jin zafin yadda ake kashe Musulmai da basu jiba basu gani ba, wadanda ke gudanar da sana’o’insu na hannu.

Mahaifin matar, Mallam Musa Wakili, ya nemi hukumomi su biya shi diyya.

Kazalika mijinta, Jubril, yace yaji kamar zai haukace bayan samun labarin kisan matarsa da dukka ‘ya’yansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *