Kimanin mutum 190 ne a gidan gyaran halin Kuje suka yi yunkurin halaka Abba Kyari sakamakon jikakkiyar da suke da ita yayin da yake aikin dan sanda.

An gano cewa Abba Kyari ya karba wasu makuden kudade daga hannunsu a lokacin da ya ke aiki inda yayi musu alkawarin samar musu da kwangila.


A halin yanzu an killace shi a gidan gyaran halin kuma ana tsananta tsaro a inda yake sannan ana tunanin mayar da shi hannun jami’an DSS.

Bayanai daga majiyoyi masu karfi sun tabbatar da yadda ake barin Abba Kyari ya ga matarsa a duk lokacin da yaso kuma yake amfani da wayarsa duk da yana tsare


Kamar yadda wasu takardun cikin gida da Premium Times ta samu damar gani suka bayyana, an kai masa harin ne a 4 ga watan Mayu, watanni bayan kama Kyari da laifin safarar miyagun kwayoyi. Maharansa sun kai kimanin 190, a cewar wani jami’i, kuma da yawansu an kai su gidan yarin ne saboda harkallar miyagun kwayoyi.


Kyari, mai shekaru 47, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, wanda jami’in tsaro ne sannan hazikin kungiyar binciken sirri na sifeta-janar kafin ya kwafsa.

Da farko dai an dakatar da shi daga aikin ‘yan sanda bayan masu bincike na Amurka sun ambaci sunansa a matsayin mai hannu a sabgar damfara tsakanin kasa da kasa da sabgar damfarar Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *