Dan tsohon shugaban kasa Marigayi Janar Sani Abacha ya yi nasara a zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP na gwamna a Kano.

Dan tsohon shugaban kasa Marigayi Janar Sani Abacha, wato Mohammed Abacha, ya yi nasara a zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP na gwamna a Kano

Abacha ya samu kuri’u 736 wajen yin nasara kamar yadda jami’ar zabe, Barista Amina Garba, ta bayyana Shugaban kwamitin zaben

Mohammed Jamu, ya ce an gudanar da zabukan nasu ne bisa ka’ida tare da sahihan deleget Jami’ar zabe.

Barista Amina Garba, ta ayyana Mista Abacha a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya samu kuri’u 736 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, Sani-Bello wanda ya samu kuri’u 710.

Shugaban kwamitin zaben, Mohammed Jamu, ya ce an gudanar da zaben fidda gwaninsu bisa ka’ida tare da zababbun deleget sannan hukumar zabe ta kasa (INEC), yan sanda da Jami’an DSS suka sanya idanu.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar INEC shida da suka hada da mataimakiyar darakta da ke kula da zabe da sanya idanu kan jam’iyyu a hedkwatar INEC, Hauwa Hassan; sakataren gudanarwa na jiha, Garba Lawal; shugaban sashin shari’a, Suleiman Alkali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *