Yanzu-Yanzu: ‘Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja

Iyalan fasinjojin da aka sace yayin da suke kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun balle zanga-zanga a babban birnin tarayya ta Abuja.

Wannan ne karo na farko da ‘yan uwan wadanda aka sacen suka fito zanga-zanga tun bayan faruwar ibtila’in.

A ranar 28 ga watan Maris din 2022, ‘yan ta’adda sun kai mugun hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna kuma hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum takwas yayin da 26 suka jigata kuma aka yi garkuwa da wasu.

Iyalan sun ce zanga-zangar sun fito ta ne sakamakon barazanar da ‘yan ta’adda suka yi na cwa za su fara halaka wadanda ke hannunsu idan har ba a cika sharuddansu.

Sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, hafsoshin tsaro da kungiyoyin duniya da su kawo musu dauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *