Yan ta’addan da suka kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna sun sake wani sabon bidiyo inda fasinjojin da aka sace suka bayyana halin da suke ciki.

Cikin wadanda suka yi jawabi a bidiyon akwai dan kasar Pakistan wand ayazo aiki Najeriya. Dan kasar Pakistanin mai suna Abu Zayd Muhammad yace:


“Ni ma’aikacin Jmarine ne a nan Najeriya, ni dan kasar Pakistan ne, an sacemu ne ranar 28 Maris a jirgin Abuja-Kaduna, mu 62 ne kuma halin da muke ciki babu kyau. Muna kira ka gwamnatin Najeriya da na Pakistan da sauran kasashen duniya su kawo mana dauki.”

Yan ta’addan sun yi barazanar fara kashe wadanda suka kwashe idan gwamnatin tarayya bata saki yaransy dake hannunta ba. Shugaban yan ta’addan, Abu Barrah, yace gwamnati ta ajiye ‘yayansu a gidan marayu dake Yola.

Ku kalli bidiyon:

https://fb.watch/ddSHDwAr8l/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *