A kasar Kamaru, wasu mazauna unguwar Dikolo dake birnin Duwala sun fusata kan abin da suka kira rashin adalci da aka nuna musu, sakamakon fitar da su daga gidajensu da karfin tuwo tare da rusa su.
A ranar 19 ga watan Mayu ne daruruwan mazauna unguwar ta Dikko suka wayi gari cikin lamarin na tashin hankali, bayan da wani kamfani mai zaman kansa da yace ya samu izini daga gwamnati ya afkawa gidajen.
Kimanin gidaje sittin aka rusa a dededdiyar anguwar dake cibiyar cinikayyar kasar Douala.
Dan kwangilar da ya jagoranci rusa gidajen, ya yi ikirarin sayan su daga hukumomi domin gina katafaren otel a can.
Charles Lotine, wani matsahi dake rajin kare hakkin wadanda aka kwace musu gidajen da karfin tuwo, yasha alwashin daukar matakin shari’a har zuwa kutun duniya.
Ko da yake wasu na kallon matakin amatsayin wani shiri na zamanantar da unguwar.