Kungiyar Kiristocin Najeriya, shiyyar jihar Kaduna (CAN) ta yi Alla-wadai da kisan wata mata yar Arewa mai juna biyu tare da ‘yayanta hudu a jihar Anambra.

Kungiyar Kiristocin Najeriya, shiyyar jihar Kaduna (CAN) ta yi Alla-wadai da kisan wata mata yar Arewa mai juna biyu tare da ‘yayanta hudu a jihar Anambra, Kudu maso gabas.

Tsagerun yan bindiga da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne suka kai farmakin inda suka hallaka mutane 12 ciki harda matar mai tsohon ciki, da yaranta su hudu.

Wannan lamari ya faru ne a karamar hukumar Orumba North karshen makon da ya gabata.


Shugaban CAN na Kaduna, Joseph Hayab, ya ce ran kungiyar ya baci bisa wannan abu da ya faru, inda yayi kira ga Gwamnatin tarayya ta nemo makasan Fatima da dukkan wadanda aka yiwa kisan gilla a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *