Bidiyon ya ce jirgin ya fadi ne a wata babbar hanya da ke kusa da inda jiragen sintiri a cikin Najeriya suke tashi da sauka, wanda ke filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos.
Kamar yadda FAAN ta bayyana, wani mutum ne ya saidawa wani jirgin kuma ya na kan hanyarsa ta zuwa in da aka siye shi.
Bincike da nazarin da aka yi akan jirgin da aka yada a shafukan intanet, ya nuna tabbas sanarwar FAAN gaskiya ce, sakamakon yadda aka dauke shi ba hade wuri guda ba. Bidiyon ya kuma nuna babu fuka-fukai a jikin jirgin, wanda hakan ke nuna ainahin yadda ake safarar shi zuwa inda aka saye shi.

An wallafa ikirarin hatsarin jirgin a shafin Tiwita, ranar 24 Mayu 2022, da misalin karfe 7;30 na yamma.
Wanda ya wallafa bidiyon mai suna @IAMoluwafemi, ya yi ikirarin ”Yanzun nan irgin sama ya fado a babbar titin Ikeja”.
Amma a jawabin da hukumar ta fitar da daren talatan, ta bayyana cewa jirgin da aka gani a titi ba hadari yayi ba, ya lalace ne kuma aka sayarwa wani yana kokarin kai shi ma’ajiya.