Yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun yi barazanar fara kashe wadanda suka kwashe idan gwamnatin tarayya bata saki yaransy dake hannunta ba.
Yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun yi barazanar fara kashe wadanda suka kwashe idan gwamnatin tarayya bata saki yaransy dake hannunta ba.

Shugaban yan ta’addan, Abu Barrah, yace
Gwamnati ta ajiye ‘yayansu a gidan marayu dake Yola. Abu Barrah ya bayyana hakan ne ga Tukur Mamu, shugaban kamfanin jaridan Desert Herald. Yace: ” ‘Yayanmu guda 8 masu shekaru 1 – 7 na tsare a gidan marayu dake Jimeta, jihar Adamawa karkashin jagorancin hukumar Sojin Najeriya.”
“Sunan ‘yayanmu; Abdulrahman, Bilkisu, Usman, Ibrahim and Juwairiyyah. An kwashesu ne daga hannun matanmu a jihar Nasarawa kuma aka kaisu gidan marayu a Yola.” “Kafin mu saki fasinjojin da cigaba da aikin jirgin kasan, wajibi ne a saki ‘yayanmu.”
Ya kara da cewa idan aka saki ‘yayan na su, zasu saki fasinjoji mata kadai. Yace idan gwamnati bata sake su ba, zasu kashe fasinjojin daya bayan daya.