Dan Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) Sadiq Ango Abdullahi, ya lashe zaben fid da gwanin dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Sabon Gari a Jihar Kaduna

Farfesa Ango, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ya bayyana hakan, lokacin da yake tsokaci kan nasarar da dan nasa, Sadiq Ango Abdullahi ya samu.

Sadiq dai ya sami kuri’a 28 yayin da sauran ’yan takarar suka biyo baya.

Idan za iya tunawa An dai sace Sadiq Ango ne lokacin da mahara suka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari, sannan suka sace mutane da dama amma yan kwanakin baya aka sako shi

Tun a ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2022 ’yan bindigar suka yi awon gaba da wasu matafiya a jirgin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.