An jibge jami’an tsaro masu yawa a wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano sakamakon zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar.

Shugaban kasar dai zai kaddamar da taron makon sojojin saman Najeriya ne a nan Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa an girke jami’an tsaro a kan titin da ke zuwa fadar Sarkin Kano domin tabbatar da tsaro.
A fadar sarkin kuwa, daruruwan jami’an tsaro ne da suka hada da jami’an ‘yan sandan Najeriya, jami’an tsaro na DSS , da sojoji, ne suka jibge a kofar gidan kewaye da motocinsu, ciki har da motocin gano abubuwan fashewa.

Tuni dai shugaban kasar ya iso birnin na Kano domin wannan ziyara ta wuni guda.

A makon da ya gabata ne dai aka samu fashewar wani abu a unguwar Sabongari da ke jihar Kano wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara tare da jikkata wasu da dama.

Kwanaki biyu bayan fashewar bom din kuma, rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano wata mota makare da kayan fashewa, bindigu da alburusai.

An dai samu rashin jituwa tsakanin mazauna yankin da rundunar ‘yan sanda kan abin da ya kai ga fashewar, inda mazauna yankin suka ce harin bam ne yayin da ‘yan sandan suka ce duk wata shaida na nuna fashewar tukunyar iskar gas ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *