Rundunar haɗin gwiwa ta sojoji mai yaƙi da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi ta ce ta tarwatsa sansanin ƙungiyar 10 a arewa maso gabashin Najeriya.


Dakarun rundunar da suka ƙunshi sojojin Nijar da na Najeriya, da kuma dakarun rundunar Operation Hadin Kai ta Najeriya, sun fara aikin ne tun a ranar Talata da ta wuce.

Wata sanarwa daga kakakin MNJTF, Kanar Kamarudeen
Adegoke, ta ce dakarunsu sun gudanar da aikin fatattakar ‘yan Boko Haram a garuruwan Grada, da Kwatan Maishayi, da Daban Karfe, da Daban Gajere, da Tumbun Buhari da kuma Tunbun Abuja.

Sai dai sanarwar ta ce dakaru ba su fafata da “ƴan ta’addan” ba saboda sun gudu daga sansanonin nasu a lokacin sharar.
Ya ƙara da cewa sojoji sun yi nasarar ɗebe makamai daga wuraren, ciki har da katan-katan na kifi, da hatsi, da kuma babur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *