Kasar Rasha ta ce ta haramtawa wasu Amurkawa 963 shiga kasarta ciki har da shugaban Amurka Joe Biden.

Kasar Rasha ta ce ta haramtawa wasu Amurkawa 963 shiga kasarta ciki har da shugaban Amurka Joe Biden da sakataren harkokin wajensa Antony Blinken Haramcin tafiye-tafiye na da dan tasiri, a wani bangare dake tbbatar da tsamin dangantakar Rasha da Amurka da kawayenta tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu.

Wannan na zuwa ne yayin da Katafaren kamfanin makamashi na kasar Rasha Gazprom ya sanar da dakatar shigar da iskar gas zuwa makwabciyar kasar Finland saboda kin amincewa da biyan ta da kudin kasar ruble.

Moscow dai ta bukaci abokan cinikinta daga “kasashe da basa ga maciji ciki harda kasashe membobin EU da su rika biyan kudin cinikin iskar gas da Rubels dinta, domin kaucewa takunkumin karya tattalin arzikin da kasashen Yamma suka kakaba mata bayan mamayar Ukraine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *