Kano: “Fashewar da ta auku a shago da ke unguwar Sabon Gari ta faru ne a sanadiyyar wasu sinadarai da ake iya hada bam da su” – Rundunar ‘yan-sandan Jihar Kano

Rundunar ‘yan-sandan Najeriya a Jihar Kano ta ce fashewar da ta auku a wani shago a unguwar Sabon Gari da ke birnin a ranar Alhamis 17 ga watan Mayu, wadda ta hallaka mutum tara, ta faru ne a sanadiyyar wasu sinadarai da ake iya hada bam da su.

A lokacin da fashewar ta auku an rika yada labari masu karo da juna dangane da musabbabin abin, inda wasu ke cewa bam ne ya tashi wasu kuma ke cewa tukunyar gas ce ta mai aikin walda ta fashe a shagon.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan Sandan Jihar SP
Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2022, rundunar ta ce mutumin da yake gudanar da haramtaccen kasuwancin na sayar da wadannan haramtattun sinadarai, wadanda ake hada bam da su, da aka gano, Michael Adejo, ya mutu a fashewar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.