Rasha ta rufe hanyar shigar da iskar gas zuwa Finland, kamar yadda kamfanin samar da iskar gas na Finland ya tabbattar

Katafaren kamfanin makamashi na Rashar Gazprom, ya ce kasar Finland ta ki cika umarnin Rasha na biyan kudin man da ta ke saya da kuɗin Rubble na Rasha, maimakon duro da dala.

Kasashen turai na na adawa da matakin na Rasha inda ta dage sai sun biya ta da kudin ƙasarta don kaucewa kawo cikas ga tasirin takunkuman da tuni aka ƙaƙabawa Rasha.
Ƙasashen Bulgaria da Poland sun fuskanci hukunci irin wannan daga gwamnatin Moscow,saboda sun bijirewa biyan kudin na Rasha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *