Majalisar dokokin jihar Yobe ta karyata batun yunkurin sauke Gwamna Mai Mala Buni.
Yan majalisar a wani taron tattaunawa da aka yi a Damaturu sun kuma yi barazanar daukar mataki na doka kan mawallafin rahoton, wato NEWS NET GLOBAL kan rahoton da ya bayar.
Mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan kafofin watsa labarai, Abdullahi Bazua ya ce zagin ba komai bane face kanzon kurege, mara tushe.
Ya bayyana cewa majalisar na da cikakken karfin gwiwa kan Gwamna Mai Mala Buni da tsarin shugabancinsa.