Tsohon Shugaban Kasa,Cif Olusegun Obasanjo, yace Najeriya na bukatar shugaba mai kishi don dora kasarnan kan turba mai kyau.

Obasanjo, ya bayyana hakan ne lokacin daya karbi bakuncin mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen, a gidansa da ke Abeokuta, a Jihar Ogun a ranar Alhamis.

Ya koka kan halin da ake ciki a Najeriya, inda ya dora alhakin da ake ciki ga kansa da kuma sauran ’yan Najeriya dake son ganin kasar ta inganta.

Tsohon Shugaban Kasar ya ce Najeriya zata iya shawo kan matsalolin tsaro a cikin shekara biyu tare da shugaban da zai iya yanke hukunci mai tsauri.

A dan haka ya bukaci ’yan Najeriya dasu jajirce su kuma kasance a shirye wajen sadaukar da abubuwa don mayar da kasar kan turba mai kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *