Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, yace ba’a matsayin dan takarar yankin Arewacin Najeriya ya fito neman kujerar shugaban kasa ba.

Ahmad Lawan ya ce yana neman kujerar shugaban kasa ne saboda ya yi amanna yana da duk kwarewar data dace ya zama shugaban kasar Najeriya domin dorawa akan bagarorin data samu nasarori.

Ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar daya gana da ’yan jam’iyyarsa ta APC, musamman wakilai a Jihar Katsina, a ranar Alhamis.

A karshen watan Mayun nan da muke ciki ne Jam’iyyar APC zata gudanar da zaben fitar da dan takarar shugaban kasarta, tikitin da kusan mutune 25 ke nema a jam’iyyar.

Lawan, wanda dan Majalisar Dattawa ne tun daga a shekara 1999, yace yana da nagarta da kwarewar da zata bashi fifiko akan sauran abokan fafatawarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.