Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana damuwar ta akan yadda kungiyoyin ta’addanci suke ta aiwatar da harkokinsu a cikin jihar.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana damuwarta akan yadda kungiyoyin ta’addanci suke ta aiwatar da harkokinsu a cikin jihar.

Yayin gabatar da rahotannin watanni hudu na farkon shekarar 2022 ga majalisar tsaron jihar, Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan ya ce yan kungiyar Ansaru da Boko Haram sun baje kolin ta’addancinsu a Birnin Gwari da karamar hukumar Giwa.

Aruwan ya ce wasu ‘yan ta’adda sun fara jan ra’ayin mazauna kauyaku da kyautuka yayin da su ke horar da su akan ta’addanci.

Gwamna El-Rufai ya nuna damuwarsa, akan yadda ‘yan ta’addan su ke matsowa daga yankin Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma don ci gaba da baje kolin ta’addanci.

Ya kara da cewa wadanda su ka kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ma ‘yan ta’addan Boko Haram ne.

Gwamnan ya kara da bayyana damuwarsa karara akan yiwuwar gudanar da zaben 2023 a Jihar Kaduna in har ba a kawo garanbawul ga matsalar tsaro ba.

Sai dai Aruwan ya ce wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne sun halaka fiye da mutanen 360 daga watan Janairu zuwa Afirilu.

Mazabar Kaduna ta tsakiya ta fi ko wanne yanki fuskantar ta’addanci inda mutane 214 su ka rasa rayukansu kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *