Dan Najeriya Da Ya tashi Daga Landan a babur Ya Bayyana Ranar Da Zai Iso Jihar Legas

Wani mutumi ‘dan Najeriya, Kunle Adeyanju, wanda yayi tafiya mai nisan gaske inda yayi burin tafiya daga London zuwa Legas a kan babur ya bada labarin yadda tafiyarsa take kasance kuma ya bayyana ranar da zai iso jihar legas.

Duk da kalubalen da ya fuskanta a kwanakin baya, Kunle a wani rubutu a ranar Alhamis, 19 ga Mayu, ya ce zai isa jihar a ranar Laraba, 25 ga Mayu.

Mutumin ya sa mutane da dama suna yin tambayoyi kan yadda zai kai ga cimma hakan tun da ko Ghana bai kai ba.

Kunle na tattakin ne domin tara kuɗi da zai tallafawa yaqi da cutar shan inna sannan ya taimaka wajen samar da tsafta. Yana ƙoƙarin tara naira miliyan 20.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *