Rikici ya barke tsakanin ‘yan acaba da ‘yan sanda a jihar Legas

An shiga tashin hankali a karamar hukumar Ojo da ke jihar Legas kan yunkurin da ‘yan sanda ke yi na tilasta dokar gwamnatin jihar ta hana acaba a wasu yankunan jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin jihar ta fitar da dokar hana zirga-zirgar ‘yan acaba a kananan hukumomi shida na jihar sakamakon kisan wani mawaki mai suna David Imoh a Lekki.

An ce an samu labarin cewa ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Onireke, Ojo, sun damke wasu baburan acaba da ke aiki a kan hanyar Mile 2 zuwa Badagry, matakin da ‘yan acaban suka bijirewa.

An shiga tashin hankali a karamar hukumar Ojo da ke jihar Legas kan yunkurin da ‘yan sanda ke yi na tilasta dokar gwamnatin jihar ta hana acaba a wasu yankunan jihar.

Yan acaban sun yi yunkurin mamaye tashar tare kokarin kubutar da wasu daga cikin mambobinsu da ‘yan sandan suka kama. Sun banka wuta a tsakiyar titi, yayin da wasu masu ababan hawa suka bar ababen hawansu a gefen titi sakamakon rikicin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *