NERC: “ba zamu kara farashin wutan lantarki ba”.

Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC ta yi fashin baki kan zaman sake duba harkar wuta da ta jagoranta, inda tace hakan ba ya nufin za’a kara farashi.

Hukumar ta bayyana hakan ne a jawabin da ta fitar ranar Talata kan bitan wata shida-shida da aka saba kan kamfanonin da aka ba lasisi.

A cewar NERC, an yi fashin bakin ne bisa jita-jitan dake yawo cewa kamfanonin rarraba wuta sun kara farashin lantarki.

Hukumar ta sanar da cewa bisa dokar sashen wuta Electric Power Sector Reform Act, EPSRA, zata fara zaman nazarin MYTO na 2022 a watan Yuli. Hukumar tace za’ayi nazari da bitan ne don ganin irin sauye-sauyen da aka samu wajen samar da wutan lantarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *