Babban Kwamandan Hukumar a Jihar, Dr. zharun Ibn Sina ne ya bayyana hakan, kamar yadda Kakakin hukumar, Lawan Ibrahim Fagge ya sanar.
Ibn Sina ya kuma ce kaso 80 cikin 100 na mutanen da za a diba za su kasance maza ne, sau kuma mata kaso 20.

Sai dai ya ce za a raba adadin da za a diba ne ga dukkan Kananan Hukumomin Jihar, inda ya ce kaso 70 cikin 100 na wadanda za a diba za su kasance cikin dakarun hukumar da aka dauka kwanakin baya, sai kuma ragowar 30 din da za su zama sabbin diba.
A bara ne dai Gwamnan na Kano ya amince da dibar dakaru 5,700 ga hukumar.
Babban Kwamandan hukumar ya shawarci dukkan masu neman gurbi a hukumar su tuntubi Kananan Hukumominsu na ainihi.