‘Yan bindiga sun kone ƙaramar hukuma guda da wata Kotun Majistire a jihar Anambra da daren jiya Lahadi.

Wasu ‘yan bindiga ne sun ƙona Sakatariyar ƙaramar hukumar Indemili da kuma wata Kotun Majirtire da ke cikin harabar wurin.

Wata majiya ta shaida cewa maharan sun farmaki harabar sakatariyar ne ranar Lahadi da daddare kuma suka aikata wannan ta’adi. Bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun ƙone fayil-fayil da wasu kadarori a wurin, har da ginin Sakatariyar.

Bidiyo da hotunan harin da ke yawo a Intanet sun nuna cewa baki ɗaya Sakatariyar ta kone a harin. Haka nan kuma, Motocin da aka aje a harabar Sakatariyar ƙaramar hukumar sun ƙone kurmus sanadin harin na daren Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *