Yajin aikin ASUU: Malaman jami’a sun ce har yanzu basu cimma matsaya da gwamnati ba, don haka babu ranar janye yajin aikin.

Rahotanni na nuna cewa har yanzu, an kasa cimma matsaya tsakanin ƙungiyar Malaman Jami’oi da gwamnatin Tarayya, kan yajin aikin da ƙungiyar ta shafe matanni tana yi.

Tun watan Fabrairun 2022 ASUU ta shiga yajin aiki, haka ma ƙungiyar ma’aikatan jami’a sun shiga nasu yajin aikin daga baya kan wasu buƙatu da ƙungiyoyin suke son gwamnati ta cika masu.

Rahotanni sun ce ɓangarorin sun tattauna a ƙarshen mako. Amma babu wata matsaya da aka cimma tsakanin Shugabannin ƙungiyar malaman ASUU da kungiyar SSANU da NASU da kuma ɓangaren gwamnati, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shugabannin ASUU sun ce gwamnati ta yi masu alkawali tun watan Disamban 2020 amma har yanzu babu abin aka yi, a cewarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *