Yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna sun sako wata mata mai juna biyu da suka sace

Wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Ansaru ne da suka kai harin nakiya a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama sun sako wata fasinja mai juna biyu.

A cikin wani faifan bidiyo da Daily Nigerian ta samu, matar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattauna da ‘yan ta’addan domin ceto rayukan wasu da ke tare da su.

Ta ce wadanda suka yi garkuwa da su na kula da su, suna ciyar da su da kyau har ma da ba su magunguna. An ruwaito daga majiyar tsaro cewa ba a biya kudin fansa ba domin a sako ta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar ta kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa wata mata ta haihu a hannun ‘yan ta’addan.

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin sakin fasinjoji sama da 60 da aka yi garkuwa da su a ranar 28 ga Maris, 2022, amma har yanzu yawancinsu suna hannunsu.

An bayar da rahoton cewa an sako mutum biyu bayan makudan kudin fansa.

Wadanda aka sako – Manajan Daraktan Bankin Noma, Alwan Hassan da dan kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, sun shafe makonni a hannunsu.

‘Yan uwan sauran fasinjojin da suka rage a sansanin ‘yan ta’adda sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi kokari saki ‘yan uwansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *