Farfessa Yemi Osinbajo ya kwatanta kisan dalibar Kwalejin Ilimin Shehu Shagar a matsayin abu mai ban takaici

Ya nuna alhininsa ne yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a bangaren jirgin shugaban kasa da ke filin jirgin Nnamdi Azikwe a Abuja, bayan dawowarsa daga Uyo, Jihar Akwa Ibom.

Ya kuma bayyana jin dadinsa akan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sultan din Sokoto su ka nuna rashin jindadinsu akan lamarin.

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, ya kada baki inda ya ce:

“Bari in fara da cewa, shugaban kasa ya nuna rashin jin dadinsa akan aukuwar wannan lamarin ta wata takarda wacce ya saki. “Zan iya cewa abin akwai ban takaici, tare da taba zuciya, irin wannan kisan wulakanci da matasa su ka yi bayan daukar doka a hannunsu; gaskiya wannan abu be yi dadi ba..

“Yadda gwamnatin Jihar Sokoto da Sultan su ka nuna bacin ransu ma sun kyauta kwarai. Ina kyautata zaton nuna bacin ransu da su ka yi da sauran miliyoyin ‘yan Najeriya ma ya nuna rashin dacewar aika-aikar. Kuma muna fatan za a yi gaggawar hukunta wadanda su ka halaka ta.”

Osinbajo ya kwatanta rashin dacewar yadda matasan su ka dauki doka a hannunsu kasancewar akwai hukumar da ya dace a kai wa kara. Ya mika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwan mamaciyar tare da fatan Ubangiji ya ba su hakuri.

Ya ci gaba da cewa:

“Ina tunanin irin tashin hankalin da ‘yan uwanta su ka shiga bayan samun labarin mutuwarta da kuma aika-aikar da aka yi mata. “Hakika abin akwai taba zuciya. Mu na yi musu ta’aziyyar tare da fatan Ubangiji ya sanya musu salama a zuciyoyinsu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.