Yayin da zaben 2023 ya karaso,Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya ta na bincike a kan jam’iyyun PDP da APC

Premium Times ta fitar da wani rahoto na musamman da ya bayyana cewa hukumar ta na binciken wasu kudi da suka shiga asusun PDP da APC Shugaban sashen gudanarwa na hukumar EFCC ta kasa, Michael Wetkas ya aika takarda zuwa ga shugabannin wasu manyan bankuna biyu da su ke Abuja.

Wadannan wasiku sun shigo hannun jaridar, inda aka fahimci jami’in hukumar ya sanar da bankunan cewa ana binciken kudin da suka shigo masu.

EFCC ta sanar da bankunan cewa akwai wasu akawun 14 da ake bincike a kansu. Akawun din na jam’iyyun siyasar ne da wani kamfani mai alaka da PDP.

Ana binciken wasu akawun

Kamar yadda rahoton ya bayyan akawun uku da aka samu daga daya daga cikin bankunan na jam’iyyar APC ne; 0692988080, 0035644896 sai 0044183689.

Akwai wani akawun mai lamba 0054586830, wanda aka sakatariyar jam’iyyar PDP ta mallaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *