Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi.

Gwamna Aminu Tambuwal ya umurci ma’aikatar ilimin gaba da sakandare da sauran hukumomin da abin ya shafa da su fara bincike kan kashe wata dalibi a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto.

Rahotanni a baya sun rawaito cewa, an samu tashin hankali daga dalibai a kwalejin na Sokoto, biyo bayan da wani sakon sautin murya ya yadu kan yadda dalibar ta zagi Annabi Muhammadu SAW a kafar sada zumunta

Daliban da suka fusata sun tarfa dalibar, inda suka kashe ta tare da kona gawarta a harabar jami’an tsaron makarantar bayan da suka yi galaba a kan jami’an tsaron makarantar da ke boye da ita.

Deborah

Bayan haka, gwamnatin jihar ta ba da umarnin rufe cibiyar har abada, kana Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai da wannan aika-aika da daliban suka aikata, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Da yake jawabi a taron manema labarai, Kwamishinan Yada Labarai na jihar Sokoto, Isa Bajini-Galadunci, ya ce Gwamna Tambuwal ya bukaci ‘yan jihar da su kwantar da hankalinsu kana su kasance masu bin doka da oda.

Ya kuma tabbatar musu da cewa za a dauki matakin da ya dace bayan binciken.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *