Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.
Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.
Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:
“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya”.
Sai dai bayan wasu musulmai na arewa sun fara barazanar cewa ba za su zabe shi ba idan PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takara, Atiku ya janye furucinsa.
Daga bisani Atiku ya goge wallafar da ya yi da kuma barazanar da aka dinga yi masa karkashin wallafar. Sannan ya yi wata wallafa da harshen Hausa wacce ya nisanta kansa daga wallafar ta farko.
Kuma a cewarsa duk wallafar da aka yi a shafukan sada zumuntarsa wacce ba ta zo da A. A. ba, ba shi ya rubuta ba.
“Cikin wannan dare na samu bayanin cewa anyi wani rubutu da babu amincewa da umarni na. Da wannan nake amfani na sanar da cewa duk wani rubutu da babu alamar AA ba daga wajena bane. Allah ya kiyaye – AA”, in ji shi.