An kama Kansila a hanyar kaduna zai ka wa ‘yan ta’adda bindigogi AK-47.

An kama wani kansila mai wakiltar Kinkiba a karamar hukumar Soba a Kaduna, Abdul Adamu Kinkiba, da bindigu AK-47 a hanyarsa zai kai wa ‘yan ta’adda bindigogi a cikin wani daji da ke jihar.

A wani rahoto da jaridar Leadership ta wallafa, jami’an ‘yan sandan  na 47 MPF Squad ne suka kama Kinkiba da ke aiki a yankin Galadimawa na karamar hukumar Giwa ta jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa an gan shi a kan babur, inda aka tsayar dashi, su yi masa tambayoyi. A cewar wani dan banga a ungwar, wanda ake zargin, wato Abdul Kinkiba ya ce wani ne ya ba shi bindigar wanda ya ki a ambaci sunansa ya kai shi ga wani mutum da ya ce shi ma bai san sunansa ba.

Majiyar wato dan bangan ya ce Kinkiba ya amsa cewa an bukaci ya tsaya bayan gadar da ke kusa da dajin Galadimawa (wani maboyar ‘yan bindiga ne) kuma wani zai fito ya karbo masa bindigar.

Shugaban Majalisar ya tabbatar da cewa mutumin kansila ne.

Tuni dai aka mika wanda ake zargin zuwa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna domin ci gaba da yi masa tambayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *