2023: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fice Daga Jam’iyyar APC.

Nura Dankadai, tsohon kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kudi na Kano ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a kasa.

Dankadai ya sanar da ficewarsa ne cikin wasikar da ya aike wa shugaban APC na mazabarsa ta Tsohon Gari a karamar hukumar Tudun Wada Tun a watan Afrilu ne ya yi murabus daga mukaminsa don ya mayar da hankali kan takarar da zai yi na kujerar majalisa ta Tudun Wada/Doguwa.

An ruwaito cewa ya sanar da hakan ne cikin wasikar da ya aike wa shugaban APC na mazabar Tsohon Gari a karamar hukumar Tudun Wada a Kano.

Ya nuna sha’awar yin takarar kujerar majalisa na wakilcin mazabun Tudun Wada/Doguwa na Kano. Duk da cewa bai sanar da jam’iyyar da za shiga a gaba ba, ana yada jita-jitar cewa zai iya koma wa jam’iyyar New Peoples Party, NNPP, wacce tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ke yi wa jagora.

Leave a Reply

Your email address will not be published.