Kimanin awa 48 bayan ya nesanta kansa da wasu kungiyoyi da suka siya masa fom din takarar shugaban kasa na 2023, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yanke shawarar fitowa takarar shugaban kasa, rahoton NAN.
A ranar 9 ga watan Mayu, Jonathan ya yi watsi da tikitin takarar da aka siya masa yana mai cewa ba da saninsa ko izininsa aka siya ba don haka bai aike su ba.
Rahotanni sun bayyana cewa ya ce cin mutunci ne wasu mutane su siya masa fom din takara ba tare da saninsa ba amma kuma yanzu tsohon shugaban kasar ya yi mi’ara koma baya kan batun.
Wata kwakwarar majiya na kusa da Jonathan, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce tabbas tsohon shugaban kasar ya shiga APC, kuma ya yi rajista a mazabarsa ta Otuoke a Bayelsa.
Majiyar ta ce ana tsammanin Jonathan zai cika fom din da kungiyar fulanin suka siya masa a ya kuma mika a ranar Alhamis.
A cewar majiyar, tsohon shugaban kasar ya samu goyon bayan isasun deleget din APC daga jihohi 36 da babban birnin tarayya, Abuja.