Gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya yanke shawarar raba kafa gabanin fidda gwani da babban zaben 2023.

Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya karbi fom din takarar Sanata mai lamba 9498 a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamnan wanda ya karbi fom din sa a ranar 10 ga Mayu, 2022, zai tsaya takarar dan majalisar dattawa ta mazabar Arewa a jiharsa inda zai fafata tare Orim Martin Ojie wanda ya karbi fom a ranar 6 ga Mayu, 2022.

Gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya yanke shawarar raba kafa gabanin fidda gwani da babban zaben 2023

Jaridar ta ruwaito cewa wasu gungun mutane da aka fi sani da ‘ya’ya maza da mata na Kuros Riba, sun saya masa fom din tsayawa takara a jam’iyyar APC domin ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamnan wanda ya bayar da tabbacin cewa zai magance matsalar rashin wutar lantarki gadan-gadan, ya ce a shirye yake ya samar da hanyar da za ta iya magance matsalar gaba daya kowa ya huta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *