Daliban kwalejin ilimin Shehu Shagari sun kashe daliba kan zargin batanci ga Annabi.

An kashe wata dalibar mai suna Deborah a kwaljin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi).

Rahotanni daga Sokoto na cewa an kashe dalibar bayan an bukaci ta janye kalamanta amma taki. Rahoton ya kara da cewa wannan abu ya faru ne ranar Alhamis da safe. Yanzu dai gwamnatin jihar Sokoto ta rufe makarantar.

An tattaro cewa Deborah ta furta kalaman batancin ne a dakin kwanan dalibai sakamakon rashin jituwan da ya auku tsakaninta da wasu dalibai. Daya daga cikin daliban da ta bukaci a sakaye sunanta tace:

“An bukaceta ta janye kalamanta amma ta ‘kiya, hakan ya fusata sauran dalibai Musulmai a kwalejin.”

Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaron makarantar sun boyeta a ofishinsu amma fusatattun matasa suka fi karfinsu, suka kasheta, sannan suka kona gawarta.

Ance jami’an tsaro yanzu sun mamaye makaranta.

Kalli Bidiyon:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *