Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa karamin ministan ilomi na kasar Emeka Nwajiuba, ya yi marabus daga kan mukaminsa a yau din nan.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaben 2023 da ke tafe su mika takardan murabus dinsu kafin ko ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022
Idan za ku iya tunawa, Karamin Ministan Ilmi, Hanarabul ChukwuEmeka Nwajiuba, ya sayi Fom din takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress APC N100m a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, a hedkwatar uwar jam’iyyar APC dake birnin tarayya Abuja.
