2023: Gwamnonin PDP sun shirya ganawar gaggawa gabanin zaben fidda gwani

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun shirya yin wani taro a wani zama na hadin gwiwa a Abuja gabanin babban taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa a yau. Taron an ce zai gudana ne a masaukin Gwamnan Jihar Benue da ke Asokoro, inji rahoton Tribune Online.

Tuni dai akasarin shuwagabannin jam’iyyar na jihohi da jiga-jigai suka isa wurin taron wanda aka ce zai gudana da yammacin yau dinnan.

Babban manufar taron dai ana tunanin shi ne batun raba tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa a zaben 2023 mai cike da takaddama.

PDP ta dage taron da aka shirya yi a yau Laraba Sai dair ahoton Vanguard ya ce, shugabancin jam’iyyar PDP ya sauya jadawalin taron na kwamitin amintattu na kasa da na majalisar zartarwa ta kasa ta PDO da aka shirya gudanarwa tun daga karfe 10 na safe zuwa 2:00 na rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published.