An yi taron tsakar dare da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da shugabannin Kungiyar Fulani da ke Abuja wadanda su ka siya masa fom din takarar shugaban kasa na N100m don su tattauna su ji matsayarsa akan tsayawa takarar.
Vanguard ta ruwaito cewa yayin taron da kungiyar masu mara wa Jonathan baya a ranar Talata, 10 ga watan Mayu, ya nuna rashin jin dadinsa akan siya masa fom din takarar ba tare da an neman izininsa ba, laifin da su ka amince kuma su ka bayar da hakuri akai.
Dr. Ibrahim Abdullahi, shugaban kungiyar Fulanin ne ya bayar da hakurin. A bangarensu, makiyayan sun bayyana cewa sun yi hakan ne don nuna jin dadinsu akan yadda ya yi amfani da Naira Biliyan 60 don bunkasa ilimin Almajirai a lokacin yana mulki da kuma samar da ci gaba a fannoni daban-daban.
Majiyoyin da su ka halarci taron sun sanar da Vanguard cewa bayan sauraron matsayar makiyayan, tsohon shugaban kasar ya amince da bukatarsu ta tsayawa takara. Kuma ya ce za su ji labari mai dadi nan ba da jimawa ba, duk da dai bai sanar da lokacin da za su ji daga gare shi ba
Cikin kwanakin nan wasu magoya bayansa su ka koma mara wa Fulanin baya akan cewa ya kamata Jonathan ya cikasa fom din takarar don gudun wuce ranar da ofishin jam’iyyar ta Abuja ta shimfida. Wata majiya ta bayyana cewa:
“Ina mai tabbatar maka da cewa magoya bayan Jonathan su na ta mara masa baya akan ya tsaya takarar. Hakan ya sa wasunsu su ke ta taimaka masa wurin cikashe fom din.”