Wani babban lauya ya nemi a kara wa Buhari wa’adin mulki

Babban Lauya, kuma dattijon kasa, Cif Robert Clarke (SAN), ya yi kira da a kara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin mulki bayan kammala mulkinsa na biyu a 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Babban lauyan, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa watannin da ke gabanin zaben 2023 ba su isa su kawo karshen rashin tsaro ba, balle a iya zabe cikin kwanciyar hankali

A wani hira da yayi da maneman labarai a talabijin na Arise, Clarke ya ci gaba da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa shugaban kasa zai iya tsawaita wa’adinsa na tsawon watanni shida, tun da farko, idan yana jin cewa gudanar da zabe zai iya zuwa da tasgaro.

Ya ce ba daidai ba ne a yi imani cewa Shugaban kasa ba zai iya ci gaba da zama a karagar mulki sama da shekaru takwas na wa’adin mulki ba.

Clarke ya ce shugaban kasar na iya kara wa kansa wa’adin watanni shida domin gudanar da zabe cikin lumana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *