Sama da tubabbun ‘yan ta’adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya – Kwamandan rundunar operation Hadin Kai, Manjo Janar Chris Musa

Manjo Janar Chris Musa ya bayyana yadda mazauna yankin suka dinga taimakon sojoji, musamman yadda suka samu bayanan sirri duk da cewa akwai bangaren da aka sanya wa shamakin sadarwa.

“Muna samun bayanai da zarar abubuwa sun faru”, a cewar kwamandan. “Wani lokacin, kalubalen da muke fuskanta shi ne hanyar sadarwa kasancewar ba ko ina bane ake samun kafar sadarwar ba; amma da zarar sun isa inda za su iya tuntubar mu suna tura mana sako.

Yayin da mutane da dama su ke ganin zubar da makaman ‘yan ta’addan a matsayin nasarar yaki, wasu kuma a razane suke. Janar Musa, a bangarensa, ya yarda da ‘yan Najeriya, musamman mutanen da ke zama a yankin Arewa maso Gabas ba su da wata fargaba a ganinsa, saboda sojoji a tsaye suke kuma idansu a sanye ya ke akan ‘yan ta’addan.

Ya ce sojoji sun dade suna kawo zaman lafiya a wasu kasashen, inda ya ce za su bi irin wannan salon wurin gyara a Najeriya. Kwamandan OPH din ya ce ba komai bane don an yi fargaba amma tabbas su kwararru ne kuma ba wannan bane karonsu na farko na yin yaki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.