“Ban aike kowa ya siya fom din takara da suna na ba” – Dr Goodluck Ebele Jonathan yayin da yayi watsi da fom din takarar shugaban kasa da kungiyar fulani ta siya masa.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi watsi da fom ɗin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progresives Congress, APC, da wata kungiyar magoya bayansa daga arewa suka siya masa, rahoton Daily Trust.

Jaridar The Cable ta ce Ikechukwu Eze, mashawarcin Jonathan a bangaren watsa labarai, ya bayyana hakan awannin bayan labarin cewa an siya masa fom ɗin yana mai cewa ba a nemi izinin tsohon shugaban kasar ba kuma ya dauki shi a matsayin ‘cin mutunci’.

“Muna son mu fayyace cewa Dr Jonathan bai san da batun ba kuma bai bada izini ba,” wani sashi na sanarwar ta ce. “Muna son mu bayyana cewa idan tsohon shugaban kasar na son takara zai bayyana niyyarsa ƙarara ga al’umma kuma ba zai shiga ta bayan gida ba.”

A baya-bayan nan dai an yi ta kira da Jonathan ya shiga takarar shugaban kasar amma ya umurci magoya bayansa su jira.

Zan fito fili karara in sanar da takara ta idan na yi shawarar yin hakan – Dr Jonathan

“Duk da muna godiya bisa goyon baya da yan Najeriya da dama ke nuna masa ya fito takarar shugaban kasa a 2023, har yanzu bai riga ya amsa kirar ba,” a cewar Eze. “Siyan fom din takarar shugaban kasa da sunan Dr Jonathan ba tare da izinin sa ba, duba da matsayin da ya rike a kasan nan cin mutunci ne. Don haka ana kira ga al’umma su yi watsi da batun.”

Hadakar kungiyoyin arewa ne suka siya wa tsohon shugaban kasar fom din takarar kamar yadda suka sanar da yan jarida a Abuja. Sanye da huluna ‘face kap’ dauke da rubutun ‘kayi takara Jonathan, kayi takara’ mambobin kungiyoyin sun ce Jonathan ne mutumin da ya fi dacewa ya yi takarar shugabancin kasa bayan Muhammadu Buhari. Tsohon shugaban kasar ya bar wa cikinsa abin da zai yi bayan watsi da tayin da aka masa.

Siyan fom din shine abu na baya-baya da aka yi don janyo hankalinsa ya shiga takara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *