Tsohon kakakin majalisar dokokin Kano, Kabiru Rurum ba shi da amfani a APC – Fa’izu Alfindiki

Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, Fa’izu Alfindiki ya bayyana tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum a matsayin ɗan siyasa marar amfani a cikin jam’iyyar APC.

Fa’izu Alfindiki, wanda shi ne kakakin ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ƙasa reshen jihar Kano, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, jim kaɗan da sanarwar da Kabiru Rurum ɗin ya bayar akan ficewarsa APC ɗin.

As as as!!! Daman ba ka da amfani a wannan tafiyar abinda ka sa ni haɗa makirci da sharri da ƙage. Kana ganin shi zai ba mu tsoro?@Kabiru Rurum” In ji Fa’izu Alfindiki.

Fa’izu Alfindiki dai yana daga cikin ƴan gaba – gaba a jam’iyyar APC Gandujiyya, kuma ya yi fice wajen kare martabar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

A jiya ne dai Kabiru Alhassan Rurum, wanda shi ne ɗan majalisar wakilai mai wakilatar ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, kuma ɗaya daga cikin masu neman jam’iyyar APC ta sahale masa takarar gwamnan Kano, ya sanar da ficewarsa daga jami’yyar APC.

Rurum ya ɗauki matakin ficewar ne bayan da matakin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, na zaɓar mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai gaje shi a babban zaɓe na 2023.

Turawa Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *