Rikicin APC a Kano: Ganduje ya shawo kan daraktan kamfen din Tinubu, a yi sulhu bayan ficewar sa daga jam’iyyar APC.

A jiya ne daraktan kamfen din takarar shugaban kasa na Bola Ahmed Asiwaju Tinubu, Abdulmumini Jibrin Kofa ya amince da shirin sulhu da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya gabatar.

A kwanakin baya ne Jibrin ya bayyana ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, sakamakon rikicin zaben neman kukerar majalisar wakilai na 2023 ta mazabar Kiru/Bebeji, jaridar punch ta ruwaito.

Gwamna Ganduje, ya umarci sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar da ta gaggauta daukar matakai na warware sabanin da ke faruwa a cikin gida da ke tasowa daga masu sha’awar tsayawa takara a mazabar Kiru/Bebeji ta tarayya.

Don haka, nan take sakatariyar jam’iyyar ta bi umarnin ta kuma kira taron masu ruwa da tsaki domin tattauna lamarin a mazabar.

A bisa umarnin gwamnan, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, ya aike da goron gayyata ga masu neman mukamin. Ya kuma yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna da su kwantar da hankula tare da ba jam’iyyar hadin kai da nufin magance rikicin a cikin gida. Ya ce ganawar za ta fito da matsaya da dukkan masu son tsayawa takarar za su amince da ita.

An tattaro cewa Abdulmumini Jibrin Kofa ya amince da sulhun jiya a taron da aka yi a bisa umarnin gwamnan.

Kofa wanda ya amince da yunkurin sulhun da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi, ya ce, “A shirye nake a yi zaman tattaunawa”, inji Daily Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *