An gurfanar da faston da ya nemi mabiyansa su biya N310,000 kudin shiga aljannah.

Wata kotu a jihar Ekiti ta bayar da belin wani malamin addini da ya so damfarar mabiyansa, Fasto Noah Abraham Adelegan.

Wata kotun majistare ta jihar Ekiti da ke zama a Ado-Ekiti ta bayar da belin Fasto Noah Abraham Adelegan na cocin Christ High Commission Ministry, Omuo Oke-Ekiti.

Fasto Abraham shine malamin addini wanda ya fada ma mabiyansa cewa yana iya kai su aljannah, yana mai cewa Omuo-Ekiti ne kofar shiga aljannah, Daily Trust ta ruwaito.

Tuhumar da akayi masa ya zo kamar haka:

Cewa kai Fasto Noah Abraham Adelegan a ranar 27 ga watan Afrilu, a Omuo Oke-Ekiti a yankin Omuo, ta hanyar karya da niyar zamba, ka gabatar da kanka ga taron jama’a a cocin Christ High Commission Ministry, Omuo, Oke-Ekiti, a matsayin wanda zai iya kaisu aljannah kafin tashin duniya idan suka biya kudi daga N300,000 zuwa N310,000 kwannensu.”

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Johnson Okunade, ya ce laifin ya saba wa sashe na 416 na dokar laifuka ta jihar Ekiti na shekarar 2012.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *