Wani Malamin addinin musulunci ya buƙaci kotu da kada ta sake shi daga gidan yari duk da cewa an wanke shi daga laifukan ta’addanci.

Kotun da ke babban birnin ƙasar ta ba shi damar ci gaba da zama a gidan yarin na tsawon kwana 30.

Rahotanni sunce Guyo Gorsa Buru dan kasar kenya ya ce yana fargabarza a iya sace shi ko kashe shi da zarar an sako shi kamar yadda ake zargin ya faru da wasu da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci.

An kama shi ne a 2018 kuma an tuhume shi da mallakarabubuwan da ke nuna yana da alaƙa da ƴan ta’adda da kuma haɗa kai da mayakan al-Shabab na Somaliya.

Lauyansa ya roƙi kotun ta ba shi tabbaci na kariya idan har an sake shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *