Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa EFCC Na Bincika Kudaden da ‘yan takara suka yi amfani Da Su Wajen Siyan Fom Din takarar – Bawa

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na kokarin ganin an halasta kudaden da aka yi amfani da su wajen siyan fom din tsayawa takara gabanin zaben 2023.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a wata hiran da ya yi ds manema labarai a gidan Talabijin na Channels TV’s “Yau, a siyasa”.

Ya ce: “Idan ana maganar sa ido kan kudaden zabe da kuma kudaden ‘yan takara, hakan yana da nasaba da aikin INEC a wannan fanni amma, ba shakka muna aiki kafada da kafada da INEC da sauran hukumomin da ke da alaka a wannan fanni. don tabbatar da cewa mun bi kudin, mun san madogara, ko halas ne ko kuma ba bisa ka’ida ba domin abin da ya shafe mu ke nan,” in ji shi a lokacin shirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.