Hukumar Kwastam ta Zone A ta sanar da kama buhunan shinkafa 7,259 na kasar waje mai nauyin kilogiram 50, kwatankwacin manyan motoci tireka 12 a watan Afrilun 2022.

Hukumar ta ce, jami’anta sun kama wasu mutane 12 da ake zargi da shigo da haramtattacciyar shinkafar da sauran kayayyaki.

Da yake zantawa da manema labarai a sashin a jiya Alhamis, Kwanturolan Hukumar Kwastam mai kula da sashin, Hussein Ejebunu ya bayyana cewar an gano buhunan shinkafar da basu dace da cin dan Adam ba.

A cewar Ejebunu, an kama mutane 12 da ake zargi da aikata wasu laifuka daban-daban da suka saba da ka’idojin hukumar kwastam.

Ya ce binciken dakin gwaje-gwaje na hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta gudanar ya tabbatar da cewar shinkafar tana da illa kuma tana dauke da wasu sinadarai masu guba da bai kamata dan Adam ya ci ba.

Ejebunu ya gargadi ‘yan Najeriya dasu lura da wasu buhunan shinkafa da ake shigowa dasu na kasashen waje, yana mai cewar ba suda dace ga cimar dan Adam ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *